Tsohon shugaban Iran Akbar Hashemi Rafsanjani ya rasu

Iran

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Akbar Hashemi Rafsanjani

Tsohon shugaban kasar Iran Akbar Hashemi Rafsanjani ya rasu.

Ya rasu ne yana da shekaru tamanin da biyu a duniya.

Marigayi Ali Akbar Hashemi Rafsanjani, mai fada a ji ne a siyasar kasar tun a shekarun 1980.

A ranar Lahadin nan ne aka kai shi asibiti sakamakon ciwon zuciya.

Shi ne shugaban Iran daga shekarar 1989 zuwa 1997, amma da ya sake neman shugabancin kasar a 2005, bai yi nasara ba, inda aka zabi Mahmoud Ahmadinejad.