Sabon shugaban Ghana ya wanki jawabin Bush

ghana

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Mista Nana Akufo-Addo ya wanki kalaman ne bayan an rantsar da shi

Fadar shugaban kasar Ghana ta bayar da hakuri, bayan ya bayyana cewa, sabon shugaban kasar Nana Akufo-Addo, ya wanki wani bangare na jawabin da tsohon shugaban Amurka George W Bush, ya gabatar yayin rantsar da shi.

Bayan an rantsar da shi a ranar Abasar, Shugaba Nana Akufo-Addo ya yi kira ga 'yan Ghana da su zamo wadanda za a rika damawa da su, ba 'yan kallo ba, su kuma zama masu bada gudun muwa, ba kawai 'yan a bamu ba.

Wadannan kalamai dai, su ne Mista Bush ya yi amfani da su a 2001.

Mista Akufo-Addo ya kuma yi amfani da wata jimla, wacce tsohon shugaban Amurka Bill Clinton ya yi amfani da ita lokacin da aka rantsar da shi a 1993.

A watan Yulin bara, uwargidan shugaban Amurka mai jiran gado, Melania Trump, ta yi ta shan suka, bayan da aka gano ta wanki wani bangare na jawabin Michelle Obama.

Daga baya, masu rubuta mata jawabi sun bayar da hakuri.

A watan Satumba, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, shi ma ya bayar da hakuri, saboda amfani da wasu kalmomi daga jawabin shugaba Obama a 2008 da yayi.