Nigeria: 'taƙaddama kan filin jirgin Kaduna'

An soki matakin rufe filin jirgin

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

An soki matakin rufe filin jirgin

Wasu 'yan Najeriya na cewa ba su gamsu da mayar da jigilar jiragen sama ba daga Abuja, babban birnin kasar zuwa Kaduna ba bisa dalilai masu dama.

Tun dai lokacin da gwamnatin Najeriya ta sanar da karkatar da jigilar jiragen zuwa Kaduna wadda ke makwabtaka da Abujar, 'yan kasar ke ta tofa albarkatun bakinsu.

A makon da ya gabata ne dai ministan kula da zirga-zirgar jiragen sama, Sanata Hadi Sirika, ya sanar da sauya wa filin jirgin sheka na makonni shida domin yin wasu gyara-gyare a filin jirgin na Abuja.

Wakilinmu na Kaduna, Nura Muhammad Ringim ya duba mana yadda filin jirgin Iyafot din Kadunar yake watanni biyu kafin fara amfani da shi.

Ya kuma ji ta bakin wasu masu amfani da filin jirgin na Abuja da masana kan harkar zirga-zirgar jirage da ma bangaren gwamnati.

Wata fasinja ta bayyana shakkunta kan amfani da filin jirgin a inda ta ce "shin Kaduna za ta iya daukar wannan nauyi? Akwai kayan aiki a filin jirgin, misali na tashi daga nan zuwa Legas?"

Ta kara da cewa " duba ka gani ga wasu a nan suna son tafiya Abuja domin barin kasa amma ba za su samu tafiya ba, haka jirgi zai bar su a tasha. Iirn wannan ake son kwatawa nan gaba?"

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Shi ma wani fasinja ya ce " bisa dogaro da abin da muke gani, ba na tunanin hakan zai yiwu. Na farko dole mu duba tsaro da kuma ko filin zai dauki yawan mutanen da na Abuja ke dauka."

Mutane da dama dai na bayyana fargaba kan yanayin tsaron hanyar Abuja zuwa Kano.

A kwankin baya hanyar ta zama wani wuri na garkuwa da mutane da fashi da makami da kuma yawan hatsarin ababan hawa sakamakon rashin kyawun hanya.

To sai dai ministan kula da zirga-zirgar jiragen na Najeriya, Sanata Hadi Sirika, ya ce, shugaban kasar Muhammadu Buhari ya amince da fitar da kudi domin gyara hanyar.

Dangane kuma da yanayin iyafot din na Kaduna, ministan ya ce abubuwa kadan ne za a gyara domin kusan komai na aiki kamar yadda ya kamata.

Sai dai kuma masana tashi da saukar jirage, kamar Kyaftin Joji wanda ya ce ana bukatar sama wa jiragen da za su rinka sauka a filin jirgin na Kaduna man da za su sha.

A saboda haka ne ya ce dole ne sai an tayar da matatar man Kaduna wadda za ta rinka samar da man.

A watan Maris ne dai gwamnatin Najeriyar ke shirin mayar da jigilar jiragen zuwa filin jirgin saman na Kaduna.