Masar: Mutane 8 sun mutu a harin bam

Masar Sinai

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Dan harin kunar bakin wake ya hallaka mutane 8 a yankin Sinai na kasar Masar

Wani harin kunar bakin wake da aka kai a ofishin 'yansanda a yankin Sinai na kasar Masar ya hallaka akalla mutane takwas.

Cikin wadanda suka mutun har da jami'an 'yansanda biyar.

Rahotanni sun ce maharin ya abka cikin ginin da wata motar daukar shara da aka makare da ababan fashewa.

Daga bisani kuma wasu maharan suka rika harba gurneti.

Bayanai sun ce harin ya lalata ginin, tare da jikkata mutane goma ciki har da fararen hula.

Har yanzu dai babu dai wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin.

Amma masu tada kayar baya dake da alaka da kungiyar IS dai sun sha kai hare-hare a kan jami'an tsaron kasar ta Masar.