Maciji ya hana jirgin Emirates tashi daga Oman zuwa Dubai

Jirgin kamfanin Emirates

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Wasu ma'aikatan jirgin na Emirates ne suka gano macijin a cikin jirgin

An soke tashin jirgin fasinjan kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na Emirates daga Oman zuwa Dubai, bayan da wasu ma'aikatan jirgin suka gano wani maciji a ciki.

An dakatar da jirgin mai kirar EK0863 wanda ya taso daga Muscat, bayan masu lura da jakunkunan fasinjoji suka gano wani katon maciji a cikin wurin ajiyar kayayyaki.

Wata kafar yada labarai ta Dubai din ta ambato mai magana da yawun kamfanin na Emirates, na cewa an gano macijin ne kafin fasinjoji su shiga jirgin.

Sai da aka sake yiwa jirgin binciken kwakwaf kafin cigaba da gudanar da harkokin sufurin bayan sa'oi da dama.

Emirates din bai bayyyana ko wani irin maciji bane, ko kuma mai hadari ne ko akasin haka.