Hukumomi a Gambia sun rufe gidan rediyo na hudu cikin wata daya

Yahya Jammeh

Asalin hoton, REUTERS/ AFP

Bayanan hoto,

Shugaba Yahya Jammeh ya musanta nasarar dan takaran 'yan hamayya Adama Barrow duk da cewar ya yarda da shan kaye a zaben tun daga farko.

Rikicin siyasar Gambiya ya kara zurfi yayin da hukumomin kasar suka garkame wani gidan rediyo.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa Paradise FM shi ne gidan rediyo na hudu da aka rufe a cikin wannan watan.

Majiyoyi sun shaida wa AFP cewar 'yan sandan fararen kaya wadanda suka yi ikirarin cewar suna aiki bisa umurnin ma'aikatar watsa labarai sun gaya wa kafar watsa labaran ta daina aiki ranar lahadi da maraice.

Gidan rediyon ya karbi bakuncin mai magana da yawun 'yan adawa, Halifa Sallah, da kuma kakakin jam'iyya mai mulki, Yakubu Colley, domin tattauna rikicin siyasar, inji rahoton.

Kawo yanzu an rufe wasu gidajen rediyo uku daban a irin wannan yanayin a watan Janairu a inda aka kyale daya daga cikinsu, Afri Radio- ta cigaba da watsa wakoki kawai.

A cewar rahoton shugaba Yahya Jammeh yana shakku a kan nasarar da abokin hamayyarsa, Adama barrow ya yi duk da cewa ya amince da hakan da farko.

Jam'iyyar Mista Jammeh ta shigar da kara a kotun kolin kasar wadda za'a saurara ranar 10 ga watan Janairu.