An gudanar da jana'izar tsohon shugaban kasar Iran

Iran Rafsanjani

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Rafsanjani babban mai goyon bayan shugaba mai ci Hassan Rouhani ne

Duban Iraniyawa ne suka fito a Tehran babban birnin kasar Iran, don yin jana'izar tsohon shugaban kasar Akbar Hashemi Rafsanjani.

Jagoran addinin na kasar ta Iran Ayatollah Ali Khamenei ne ya jagoranci addu'ion sallar jana'izar.

Rafsanjani, wanda ya jagoranci kasar daga shekarar 1989 zuwa 1997, ya mutu ne a ranar Lahadi yana da shekara 82 sakamakon bugun zuciya.

Ya kasance daya daga cikin masu fada a ji tun bayan juyin juya halin shekarar 1979 a kasar ta Iran.

An sha sukar shi kan bakin mulki, amma kuma daga bisani ya zama mai goyon bayan masu rajin kawo sauye-sauye a salon mulki.

A ranar Litinin ne aka fara zaman makokin kwanaki uku a kasar.

Gidan talabijin na kasar ya nuna dandazon masu zaman makoki da suka mamaye kan titina a harabar jami'ar birnin Tehran, inda aka gudanar da sallar jana'izar.

An samarwa da mutane motocin safa-safa kyauta zuwa wurin jana'aizar.

An kuma daga bakaken tutoci, da wasu manyan alluna dauke da hotunan shugaba Ayatollah da marigayi Rafsanjani na murmushi tare.