'Yadda fyaɗe ke ƙara ta'azzara a arewacin Najeriya'

Rashin hukunta masu laifi ya janyo wasu ke aikata laifin
Bayanan hoto,

Ana yi wa yara maza da mata fyade

Wata kungiya mai zaman kanta da ke ayyukan kula da mata da kananan yara da marayu a jihar Kadunan Najeriya, mai suna ARRADA, ta ce, fyade na karuwa yadda ba a zato, a arewacin Najeriya.

Hajiya Rabia Ibrahim, shugabar kungiyar ta ARRADA, ta bayyana wa BBC cewa, an sami batutuwan yi wa yara maza da mata fyade fiye da 100 a shekarar 2016.

Sai dai kuma ta ce batutuwan da suka fi zafi da daukar hankalin mutane sun fi guda 50 wadanda aka samu a daga watan Agusta zuwa Disambar 2016.

Hajiya Rabia ta zayyana manyan fyaden da aka samu kamar haka

  • A Kaduna, wani dagaci mai shekara fiye da 80, ya karbi wata yarinya da ta bata kuma da shi da dansa da jikansa duka sun kwashe shekara guda suna yi wa yarinyar fyade.
  • Yaro dan shekara biyar ya gamu da ajalinsa, bayan da wani matashi mai shekara 12 ya yi lalata da shi, a Zariya.
  • Wata yarin 'yar shekara hudu ta samu matsalar kasa rike bayan gida sakamakon fyaden da aka yi mata ta gaba da bayanta.
  • An kuma sami wani magidancin da yake yi wa 'ya'yan cikinsa guda uku fyade da suka hada da mai shekara biyu da hudu da kuma 'yar wata bakwai wadda cikinta ya kumbura saboda hadiye maniyyin mahaifin nata.

Hajiya Rabia ta kuma koka kan yadda ake samun jan kafa tsakanin hukumomin 'yan sanda da bangaren Shari'a wajen hukunta masu aikata irin wannan laifi.

Ta kara da cewa rashin hukunta wadanda aka samu da laifin ne yake sanya al'amarin yake kara ta'azzara.

To amma shugabar kungiyar ta ARRADA, ta shawarci jama'a musamman iyaye kan yadda ya kamata su kula da kai komon 'ya'yansu.

  • Ya kamata iyaye musamman mata su sanya ido kan masu kula da 'ya'yansu, misali direba ko kuma mai aiki.
  • Iyaye su kula sosai da mutanen da 'ya'yan nasu suke matukar shakuwa da su misali ankul ko anti da dai sauransu.
  • Kula da masu yawan yi wa yara wasa ko kuma ba su kyaututtuka.
  • Ka da iyaye su rinka korar 'ya'yansu da su je su yi wasa domin kyale su shakata.
  • Iyaye mata su rinka duba al'aurar 'ya'yansu musamman idan suka zo suna kuka tunda dai ba sa iya magana.

Sharhi, Usman Minjibir

Kusan dai za a iya cewa matsalar fyade a arewacin Najeriya na daya daga cikin wasu matsaloli da ake samu amma kuma ba a son daga maganar.

Masana suna alakanta rashin bunta zancen fyade ga dalilai na addini da al'ada da kuma rashin son kunyata a cikin al'umma.

Sau da yawa a kan samu iyaye maza da suke yi wa 'ya'yansu 'yan mata fyade amma saboda gudun abin kunya, a kan lullube maganar.

A mafi yawancin lokaci, da zarar an daga irin wannan maganar, abin da ke biyo baya shi ne kyama daga wurin al'umma.

A kan samu yanayin ma da yarinya ba za ta samu manemi ba sakamakon fuskantar matsalar fyade duk kuwa da cewa ba a son ranta aka yi mata fyaden ba.

Ana dai ganin cewa da za a rinka kai maganar ga mahukunta kuma ba tare da wata-wata ba a hukunta duk wanda aka samu da laifi, to da al'amarin ya bai kai haka ba.

Arewacin Najeriya dai na daya daga cikin yankuna masu dimbin al'umma musulmai a nahiyar Afirka.

Kuma yankin ne yake gaba a yawan musulmai a Najeriya.

Har ma wasu jihohin yankin na ikrarin kwatanta zartar da Shari'a bisa doran AlQur'ani.