Abubuwan da na cimma a mulkina — Obama

Obama zai bar mulki ranar 20 ga watan Janairu
Bayanan hoto,

Obama ya kuma nemi jajircewar Amurkawa

Shugaban Amurka mai barin gado, Barack Obama, ya ce yana alfahari da nasarorin da ya samu a tsawon shekaru takwas da ya yi yana mulkar Amurkawa.

Obama ya bayyana hakan ne yayin wani jawabin bankwana da ya yi wa al'ummar kasar, ranar Laraba a Chicago.

Baya ga batun halasta auren jinsi guda, Obama ya ambata shirin kiwon lafiyar da ya ba wa Amurkawa fiye da miliyan 20 damar samun ingantaccen tsarin na kiwon lafiya.

Sannan kuma ya ambaci bunkasa tattalin arzikin da ya yi wanda ya ce ya yi warwas a lokacin da ya hau mulkin kasar.

Har wa yau, Obama ya yi batun yadda jami'an tsaron kasar suak samu nasara kan wadanda ya kira ''yan ta'adda', da suka hada da kisan Osama bin Laden.

Sai dai kuma mista Obama ya yi wa magajinsa hannunka mai sanda dangane da batun karuwar wariyar launin fata a kasar.

A ranar 20 ga watan Janairu ne dai Obama zai mika mulki ga zababben shugaban kasar, Donald Trump.