Nigeria: 'Yan mata sun koka kan dokar kayyade kayan aure a Kano

Zawarawa
Bayanan hoto,

Akwai alamun wasu kananan hukumomi za su biyo bayan Dambatta

'Yan mata a karamar hukumar Dambatta ta jihar Kano a Najeriya, sun ce ba su ji dadin dokar da masu ruwa da tsaki a karamar hukumar suka yi ba, wadda ta kayyade kayan aure.

A makon da ya gabata ne dai masu fada aji a Dambatta suka fidda wani kundin doka wanda ya takaita yawan wahalhalun da ake yi wajen aure.

Kundin dokar mai shafi biyar ya wallafa sabon tsarin aure kamar haka:

 • Saukaka kayan aure: Hijabi da mayafi da takalmi da jaka da sarka da warwaro da dan kunne da kuma man gashi guda biyu-biyu.
 • Saiti dai-dai na Jagira da jambaki da hoda da agogo.
 • Turare guda uku
 • Sabulu saiti uku
 • Tufafi da man shafawa kala shida kowanne
 • Akwati daya ko biyu

Dokar ta kuma haramta wasu al'adu kamar haka:

 • Zancen dare
 • Kai lefe da mata ke yi
 • Kayan sa-rana
 • Kade-kade lokacin biki da ke haifar da cakuduwar maza da mata
 • Kamun amarya da ango
 • Bayar da kudin abincin biki
 • Kai Gara
 • Budar kai
 • Da kuma hana taron motocin daukar amarya

Asalin hoton, Google

Bayanan hoto,

Dokar ta kuma hana al'adar kade-kade lokacin biki da ke haifar da cakuduwar maza da mata

Yanzu dai samari na karamar hukumar bakinsu har kunne domin sun ce abin da suka dade suna jira ne.

Wani sauraryi a garin na Dambatta ya shaida wa BBC cewa "gaskiya wannan sauki ne ya zo mana domin da akwai wani kudin uwar miji da uban miji amma yanzu duk babu wadannan."

To sai dai 'yan mata sun ce ba su ji dadin dokar ba domin a cewrsu hakan zai sanya kimarsu ta zube a idanun mazaje.

"Gaskiya ban ji dadin wannan doka ba saboda har ta kai ga samarin garin nan marasa mutunci na cewa da dubu bakwai za ka kwashi mata biyu." in ji wata mazauniyar Dambatta.

A bangaren malaman musulunci kuwa, wasu sun ce dokar ba ta dace ba domin a cewarsu babu inda aka nuna kayyade abun da za a ba wa mace lokacin aurenta.

Sharhi, Usman Minjibir

Za a dai a iya cewa ba wannan ne karon farko da wata al'umma kan kirkiro dokar takaice hidimar aure ba a arewacin Najeriya.

Garuruwa daban-daban sun sha kirkiro irin wannan dokar amma sai a wayi gari ba ta aiki.

Ko a garin Dambattan ma, an ce wannan shi ne karo na uku da ake shimfida irin wannan dokar.

Wasu dai na alakanta rashin tasirin da kokar kan yi da wuce gona da iri da masu hannu da shuni ke yi.

Yawancin lokuta, a kan fara karya irin wadannan dokokin ne daga gidajen masu fada aji da masu ido da tozali musamman a lokacin bukukuwansu ko kuma na 'ya'yansu.

Arewacin Najeriya dai na fama da matsalolin rayuwa da suka hada da talauci da yawan sakin mata al'amarin da ke janyo yawaitar yara marayu a yankin.

Sai dai kuma masu sharhi na ganin irin wannan mataki ba zai kai ga samar da mafita ba illa iyaka ma dai ya sanya maza yin auri saki.

To amma kuma wasu na ganin bisa ga dokar da al'ummar Dambatta suka fitar, akwai masu sanya ido kan yadda auren zai kasance.