'Za mu dauki mataki kan hana shigar da motoci Nigeria'

Kakakin majalisa Bukola Saraki
Bayanan hoto,

Rikicin da kudancin jihar Kaduna ke fama da shi, na sanya jama'ar yankin zaman zullumi

'Yan majalisar dattawan Najeriya sun yi watsi da wata dokar da hukumar kwastan ta kafa, wadda ta haramta shigar da motoci cikin kasar ta iyakokin da ke tudu.

Sanatocin sun soki dokar,bisa cewa za ta tagayyara dubban kananan `yan kasuwa, tare da talauta al`umomin yankin da dokar ta shafa.

Hukumar kwastam dai ta bayyana cewa ta kafa dokar ne da nufin maganin masu fataucin mota da ke zille wa biyan haraji.

'Yan majalisar sun ce za su bi duk wata hanya wajen ganin dokar ba ta yi aiki ba.

Tuni dai majalisar ta gayyaci shugaban Kwastam din, Hamidu Ali, da ya bayyana gabanta domin yin bayani kan dokar.

A farkon watan Janairun 2017 din nan ne dai dokar hana shigar da motoci ta tudun ta fara aiki a Najeriya.