Nigeria ka iya bai wa Yahya Jammeh mafaka

  • Nasidi Adamu Yahya
  • BBC Hausa
Majalisar wakilan Najeriya

Asalin hoton, Nigeria House of Representatives

Bayanan hoto,

Babu tabbas kan ko Jammeh zai amince da matakin

Majalisar wakilan Najeriya na shirin yin muhawara kan wani kudiri da zai duba yiwuwar bai wa shugaban Gambia Yahya Jammeh mafakar siyasa idan ya amince ya sauka daga mulki cikin girma-da-arziki.

Mai magana da yawun majalisar wakilan Abdulrazak Namdas ya shaida wa BBC cewa manufar kudirin dokar ita ce a samu zaman lafiya a kasar ta Gambia, wadda ta fada rikicin siyasa tun bayan da shugaba Jammeh ya ki amincewa da shan kaye a zaben da aka yi a watan Disamba.

Da farko dai Mr Jammeh, wanda ya kwashe shekara 22 a kan mulki, ya amince da shan kaye a hannun Adama Barrow, har ma ya taya shi murna.

Sai dai daga bisani ya ce ba zai sauka daga mulki ba, yana mai zargin cewa an takfa kura-kurai a zaben.

Kungiyar raya tattalin arzikin yammacin Afirka, ECOWAS ta shiga tsakani, inda ta nada shugaban Najeriya Muhammadu Buhari domin ya jagoranci yunkurin da take yi na ganin Mr Jammeh ya sauka daga mulki.

Shugaban na Gambia dai ya yi barazanar sanya kafar wando daya da ECOWAS, wacce da farko ta ce za ta yi amfani da karfin soja wajen kawar da shi daga mulki, koda yake daga bisani ta ci gaba da tattaunawa da shi domin magance rikicin siyasar kasar.

Masana na ganin wannan mataki da majalisar wakilan Najeriyar take shirin dauka ka iya yin tasiri wajen magance rikicin Gambia.

Sai dai babu tabbas ko Yahya Jammeh zai amince da matakin.