'Yan majalisar Nigeria sun yarda a bai wa Jammeh mafakar siyasa

  • Nasidi Adamu Yahya
  • BBC Hausa
Majalisar wakilan Najeriya

Asalin hoton, Nigeria House of Representatives

Bayanan hoto,

Babu tabbas kan ko Jammeh zai amince da matakin

Majalisar wakilan Najeriya ta amince kasar ta bai wa Shugaba Yahya Jammeh na Gambia mafakar siyasa idan ya amince ya sauka daga mulki ba tare da matsala ba.

A wata muhawara da suka tafka ranar Alhamis, 'yan majalisar sun goyi bayan matakin da kungiyar raya tattalin arzikin yammacin Afirka, ECOWAS ta dauka na nada shugaban Najeriya Muhammadu Buhari domin ya jagoranci yunkurin da take yi na ganin Mr Jammeh ya sauka daga mulki.

Majalisar ta umarci ministan harkokin wajen Najeriya ya tabbatar cewa Mr Jammeh ya mutunta matsayin 'yan kasar na zaben sabon shugaba Adama Barrow.

'Yan majalisar sun yi kira ga Shugaba Yahya Jammeh ya yi biyayya ga matakin da 'yan kasar suka dauka na zaben sabon shugaban kasa.

A watan Disamba ne Mr Barrow ya kayar da Mr Jammeh a zaben.

Da farko dai Mr Jammeh, wanda ya kwashe shekara 22 a kan mulki, ya amince da shan kaye, har ma ya taya Adama Barrow murna.

Sai dai daga bisani ya ce ba zai sauka daga mulki ba, yana mai zargin cewa an takfa kura-kurai a zaben.

Shugaban na Gambia dai ya yi barazanar sanya kafar wando daya da ECOWAS, wacce da farko ta ce za ta yi amfani da karfin soja wajen kawar da shi daga mulki, koda yake daga bisani ta ci gaba da tattaunawa da shi domin magance rikicin siyasar kasar.