An sabunta asibiti don yin tiyata ga 'yar Masar mai nauyin kilo 500

Eman Ahmed Abd El Aty

Asalin hoton, Dr Muffazal Makdawala

Bayanan hoto,

'Yar Masar din mai shekara 36 ta yi shekara 25 ba ta fita daga gida ba.

Wani asibiti a Indiya ya gina ɗakin tiyata don yi wa wata mata wadda ƙibarta ta kai kilo 500 aiki.

Sabon ginin da aka yi a asibitin Saifee da ke Mumbai zai kasance da dakin tiyata da kuma ɗakin kwantar da masu buƙatar matuƙar kulawa.

Ana sa ran 'yar asalin Masar ɗin, Eman Ahmed Abd El Aty, mai shekara 36, za ta sauka garin cikin jirgin shata a karshen watan Janairu.

'Yan'uwanta sun ce rabonta da fita daga gida tsawon shekara 25 kenan.

'Yan'uwan nata ne suka ba da kiyasin nauyinta.