Dole 'yan Cuba su nemi visa kafin shiga Amurka

Amurka da Cuba sun shafe shekaru suna ga maciji

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Amurka da Cuba sun shafe shekaru suna ga maciji

Amurka ta kawo karshen wata dadaddiyar manufa da ta ba wa bakin haure na Cuba wata muhimmiyar dama ta kyale su su shiga kasar ko kuma kasancewa a cikinta ba tare da takardar izinin shiga wata kasa ba wato visa.

Gwamnatin kasar Cuba ta yi korafin cewa manufar wadda akafi sani da "wet foot, dry foot," na karfafawa dubban mutane gwiwar arcewa daga kasar a kowacce shekara.

Shugaba Obama ya ce soke manufar ya zama wajibi, kuma zai kasance wani mataki na dai-daita dangantakarsu da Cuba.

Kasashen biyu wadanda suka jima suna cacar baka, sun shirya ne a shekarar 2015 bayan sun kwashe rabin karni ba sa ga maciji.