An sake cimma yarjejeniya da sojoji masu bore a Ivory Coast

Wannan ce yarjejeniya ta biyu da aka cimma a cikin mako guda

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Wannan ce yarjejeniya ta biyu da aka cimma a cikin mako guda

Gwamnatin Ivory Coast ta ce ta cimma wata yarjejeniya da sojojin da ke yin bore a kan batun biyan albashi da alawus.

An cimma yarjejeniyar ne bayan an shafe sa'oi ana tattaunawa tsakanin ministan tsaron kasar da kuma masu shiga tsakani daga bangaren sojojin, kuma wannan ce yarjejeniya ta biyu da aka cimma tsakanin bangarorin a cikin mako guda.

A yayin da ake tattaunawa domin cimma yarjejeniyar, an ji karar harbe-harben bindiga a wasu birane da ke sassan kasar ,yayinda sojojin da ke boren kuma suka kewaye Bouake inda ake tattaunawar.

Ba a bayyana bayanai game da yarjejeniyar da aka cimma ta baya ba, kuma ba bu tabbas a kan ko sojojin za su amince da wannan yarjejeniya da aka cimma yanzu ba.