Najeriya za ta sake bude matatun man ta uku bayan wasu gyare-gyare

Matatun man Najeriya ba sa aikin da ya dace
Bayanan hoto,

Matatun man Najeriya ba sa aikin da ya dace

A Najeriya ma'aikatar mai ta kasar ta bada sanarwar sake bude matatun mai na kasar guda uku.

Matatun man wadanda suka hada da matatar mai ta kaduna da ta Fatakwal da kuma ta Warri, an rufe su ne domin gudanar da wasu 'yan gyare-gyare.

A baya dai an sha rufe matatun kasar yawancin saboda rashin danyen man da za su tace sanadiyyar fasa bututun da ke kai mai zuwa matatar.

A wani lokacin dai matatun man kan tsaya cak ba sa aiki lamarin da ke sa a dauki wasu watanni ba tare da an gyara su ba, hakan ke sa a rinka shigo da man daga kasashen ketare.

Kakakin ma'aikatar man ta Najeriya, Mr Ndu Ogar Madu ya ce ba laifi ba ne idan a rufe matatu domin ayi wasu gyare-gyare, saboda injina ne matatun, to amma bisa la'akari da gyare-gyaren da akayi a yanzu,akwai tabbacin cewa matatun za su yi aiki na dogon lokaci ba tare da wata matsala ba inji Mr Madu.

Najeriya dai na daga cikin kasashen duniya da ke da arzikin mai, to sai dai kuma ana fitar da danyen man a siyo tatacce daga kasashen ketare saboda yanayin aikin da matatun kasar ke yi bai wadatar ba.