Tottenham ta casa West Brom da ci 4-0

Asalin hoton, EPA
Tottenham ta koma mataki na biyu a kan teburin Premier
Tottenham ta matsa zuwa ta biyu a teburin Premier, bayan ta mamaye karawarsu da West Brom ta hanyar casa ta da ci 4 da nema a filin wasa na White Hart Lane.
Zaratan Tottenham ɗin ba su fito da wasa ba, a ƙoƙarinsu na cin wasa na shida jere a gasar, sun kai hari 10 kuma suna da kashi 78 cikin 100 na gwanintar taka rawa kafin hutun rabin lokaci.
Kane - wanda aka yi masa haihuwa a wannan mako - ya jefa kwallonsa ta uku a raga bayan Kyle Walker ya taɓa masa.
Ɗan wasan gaban Ingilar ya kai hari sau 11, a wannan wasa da Tottenham ta yi zarra ga West Brom mai hari 8.
Gareth McAuley na West Brom ne ya ci gidansu ƙwallon farko mintuna ƙalilan da fara wasan.