Wasan Kano Pillars an tashi da taƙaddama

Kano Pillars
Bayanan hoto,

Wasan farko na Kano Pillars a gasar Firimiya ya tashi da takaddama

Kano Pillars ta ci Ifeanyi Uba 1-0, a wasanta na farko da ya kare cikin takaddama kafin minti na casa'in.

Karawar ita ce bikin bude gasar firimiyar Nijeriya ta bana, inda filin wasa na Sani Abacha da ke Kano ya cika maƙil da 'yan kallo.

Ɗan wasan gaban Kano Pillars, Gambo Muhammed ne ya jefa ƙwallo a ragar Ifeanyi Uba kafin a tafi hutun rabin lokaci.

Sai dai, taƙaddama ta taso lokacin da Ifeanyi Ubah ta samu bugun tazara, amma kafin ta buga sai alkaliyar wasa, Foluso Ajaye ta busa hutun rabin lokaci, daidai lokacin ɗan wasan Ifeanyi ya buga kwallo wadda ta faɗa raga.

'Yan wasan Ifeanyi Ubah sun ci gaba da ƙorafi kan hana ƙwallon da alƙaliyar wasa ta yi kuma ba a daɗe da komawa hutun rabin lokaci ba, sai ta kori kocin Ifeanyi Ubah daga karawar.

Lamarin dai ya harzuƙa 'yan wasan Ifeanyi inda suka dakatar da buga wasa, sannan suka ki ci gaba da fafatawar.

Alƙaliyar wasan ta jira tsawon wani lokaci ko ƙungiyar Ifeanyi Ubah za ta koma fili amma hakan ya faskara daga nan kuma sai ta busa tashi.