Najeriya: An sace dalibai da malamai a Ogun

Nigeria militants

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Wasu 'yan bindiga a kudu maso gabashin Najeria

'Yan bindiga a jihar Ogun dake kudu maso yammacin Najeriya sun sace wasu dalibai biyar da malamansu biyu daga wata makaranta ta kasa da kasa.

'Yan sanda sun ce suna kokarin ganin sun ceto mutanen.

Akasarin daliban makarantar 'yan kasar Turkiya ne.

A watan Satumba, 'yan sanda a jihar ta Ogun suka ceto wasu 'yan kasar China da aka sace, wadanda ke aiki a wani kamfanin fasa dutse.

Satar mutane domin neman kudin fansa, matsalace da ta zama ruwan dare a kudancin Najeriya, musanman a yankin Niger Delta mai arzikin mai, inda aka fi hakon ma'aikata 'yan kasashen waje.