An yi zanga-zanga a Tanzaniya kan farautar giwa

Elephants

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Giwaye a Afirka na karewa saboda yawan farautarsu da ake yi

Kimanin mutane dari biyar ne suka yi maci a Dar es Salaam, birni mafi girma a Tanzaniya, domin nuna bacin rai da farautar giwa da ake yi.

Tattakin na tsawon kilomita biyar, an fara shi ne daga ofishin jakadancin China dake birnin.

Kimanin giwaye dubu talatin ne aka kashe wa a kowacce shekara a Afirka, kuma China, ita ce babbar kasuwar hauren giwayen.

A karshen watan Disamba, Beijing ta sanar da cewa za ta hana cinikin hauren giwa daga karshen wannan shekarar.

Tanzaniya ce kasar da matsalar farautar giwa ta fi shafa, inda bincike ya nuna yawan giwayen ya ragu da kashi sittin cikin dari a tsakanin shekarar 2009 da kuma 2014.