Faransa za ta ci gaba da girke sojoji a Afirka har sai abin hali ya yi in ji Francois Hollande

Faransa na horar da sojojin Afirka fiye da dubu 20 a kowacce shekara
Bayanan hoto,

Faransa na horar da sojojin Afirka fiye da dubu 20 a kowacce shekara

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya ce kasarsa za ta ci gaba da girke sojoji a Afirka har sai abin da hali ya yi.

Mr Hollande ya ce aikin da sojojin za su yi guda biyu ne, na farko tabbatar da tsaro a Mali in da rundunar ke da sansaninta tun shekarar 2012 domin yakar barazanar musulmi masu tsatsauran ra'ayi a Mali.

Aiki na biyu kuwa da sojojin za suyi in ji shugaban kasar ta Faransa, shi ne horar da sojojin kasashen Afirka.

Kasar Faransa dai na horar da sojojin Afirka fiye da dubu ashirin a kowacce shekara tun daga shekarar 2013.

Masu sharhi dai sun ce manufar wannan shiri shi ne rage bukatar tura sojoji kai tsaye zuwa Afirka domin su taimaka musu wajen yaki da masu tayar da kayar baya.