Fursunoni sun kwace iko da gidan yari a Brazil bayan tarzoma

Ba wannan ne karon farko da aka samu tarzoma a gidan yari a Brazil ba

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ba wannan ne karon farko da aka samu tarzoma a gidan yari a Brazil ba

Wasu fursunoni sun kwace iko da wani gidan yari a Brazil, a wata babbar tarzoma da ta kasance ta uku da a kayi a kasar a cikin shekarar nan.

'Yan sanda sun ce an kashe a kalla fursunoni uku a tarzomar wadda a kayi a gidan yarin Alcaçuz da ke arewa maso gabashin birnin Natal.

Ana kyautata tsammanin an kashe wasu fursunonin da dama a rikicin da a kayi tsakanin wasu 'yan adaba da ke gaba da juna a gidan yarin.

Ana dai jiyo karar fashewar abubuwa daga wajen gidan yarin inda 'yan sandan kwantar da tarzoma ke dakon wayewar gari su shiga cikin harabar sa.

A farkon watan da muke cikin an kashe kusan fursunoni dari a irin wannan tarzoma a gidajen yarin da ke jihohin Amazonas da kuma Roraima.