Kasashe 70 sun yi taro a Paris kan Gabas ta Tsakiya

Israel

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Rabon Isara'ila da Falasdinu su yi kyakkyawar tattaunawa tun 2014

An kammala wani babban taro a Paris kan samar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya.

Taron ya sake jaddada kudurin kasashen duniya na samar da kasashe biyu, a matsayin masalaha ta magance rikice-rikice tsakanin Isra'ila da Falasdinu.

Ministan harkokin wajen Faransa, Jean-Marc Ayrault ya ce manufar taron wanda kasashe fiye da saba'in ne suka halarta, ita ce dawo da zaman lafiya a Gabas ta Tsakaiya, don kada kungiyar IS ta kara karfi.

Wakilin BBC a Paris ya ce an gudanar da taron ne, yayin da ake cike da zulumi kan manufofin gwamnatin Amurka mai jiran gado ta Donald Trump a Gabas ta Tsakiya.

Firayiministan Isra'ila ya bayyana taron a matsayin shirme.