Trump bai san ko wacece Rasha ba— Brennan

Trump

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Mista Brennan ya ce Trump bai san ko wacece Rasha ba

Daraktan hukumar leken asiri ta Amurka CIA mai barin gado, ya ce har yanzu, Donald Trump bai fahimci Rasha ba, da abinda take kukkullawa, da irin abubuwan da za ta iya yi.

John Brennan ya ce idan Mista Trump ya kama aiki, ya kamata ya yi takatsantsan game da yayewa Rasha takunkumin da aka sanya mata, sai dai in ta canja hali.

Daraktan hukumar ta CIA ya kuma soki irin sakon da Donald Trump din ke aikewa duniya, bisa yadda yake wasa da zargin da hukumomin leken asiri na Amurkan ke wa Rasha na yin kutse don ragewa zaben shugaban kasar inganci.

Ya kuma gargadi Mista Trump da ya guji bambarmar mayar da martani akan ko wane irin abu, da zai iya yiwa Amurkan illa.