Venezuela: Ana takun saka tsakanin shugaban kasa da 'yan adawa

Venezuela na fama da matsalar tattalin arziki

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Venezuela na fama da matsalar tattalin arziki

'Yan adawa a Venezuela sun zargi shugaban kasar Nicolas Maduro da saba tanade-tanaden kundin tsarin mulkin kasar ta hanyar gabatar da jawabi a kan halin da kasar ke ciki a gaban kotun kolin kasar, maimakon gaban majalisar dokoki.

A yayin jawabin nasa, Mr Maduro ya soki majalisar dokokin, wadda a makon jiya ta ce ya gaza sauke nauyin da ya rataya a wuyansa saboda barin tattalin arzikin kasar na kara tabarbarewa.

Mr Maduro ya ce yana sauke duk wani hakkin da ke wuyansa, sai dai ya ce tattalin arzikin kasar ta Venezuela wanda ya ginu a kan fitar da mai, yanzu ya yi kasa saboda faduwar farashin mai a kasuwannin duniya.