Dokar Nigeria ta durkusar da kasuwar motoci a Jamhuriyar Benin

Farashin motoci ya sauka a Cotonou saboda rashin ciniki
Bayanan hoto,

Farashin motoci ya sauka a Cotonou saboda rashin ciniki

Masu sayarda motoci a Cotonou babban birnin jamhuriyar Benin, sun koka da rashin cinikin motoci, tun bayan da gwamnatin Najeriya ta sanar da hana shigo da motoci na tokumbo daga iyakokinta na tudu.

Bincike ya nuna cewa sama da kaso casa'in da biyar na motocin tokumbo da ake sauke su a gabar tekun jamhuriyar Benin, masayansu na fitowa daga Nigeria ne mai makwabtaka da kasar.

Masu sayar da motocin sun ce yanzu kasuwar ta ja baya kuma farashin motocin ya sauko, saboda faduwar darajar Naira da kuma rufe iyakokin da Nigeriar ta yi wadanda suka taimaka wajen rashin samun cinikin motocin.

A baya dai jiragen ruwa na sauke kwantenoni ciki da motoci kamar dubu goma a wata,amma tun bayan da gwamnatin Najeriya ta sanar da sabuwar dokar,jirage a gabar tekun Cotonou suka ja baya inda a sati bai fi a sauke kwantenoni hamsin ba.

Rasa ayyuka

Karancin masu sayen motocin ya sanya wasu daga cikin masu wannan harakar rasa ayyukansu.

Majalisar Dattawan Nigeriar dai ta bukaci gwamnatin kasar da ta janye wannan matakin da ta ce ya haddasa dubban 'yan kasar sun rasa aikin yi.

To sai dai kuma hukumar hana fasakwauri ta Nigeria ta ce matakin da aka dauka zai taimaka wajen bunkasa harajin da gwamnati ke samu tare da samar da aikin yi.