An kai hare-haren bam cikin harabar jami'ar Maiduguri

Maiduguri
Bayanan hoto,

Karon farko kenan da aka kai hari jami'ar Maiduguri a cikin shekara 7

Bama-bamai sun fashe wayewar garin ranar Litinin a harabar jami'ar Maiduguri.

Lamarin ya faru ne a wani ƙaramin masallaci da ke harabar Jami'ar da asubahin ranar Litinin da kuma wani a kusa da wata ƙofar jami'ar.

Wani shaida ya ce ɗan ƙunar-bakin wake ne ya kai harin a wajen harabar masallacin, kuma wani Farfesan jami'ar na daga cikin waɗanda suka mutu.

Ma'aikatan agaji sun tabbatar da kwashe gawawwaki, ciki har da ta Farfesa da wani yaro da kuma mutanen da suka kai hare-haren.

Bayanan hoto,

Jami'ai suna bincike a ɗaya daga cikin wurin da abin ya faru

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya yi Alla-wadai da hare-haren da aka kai jami'ar Maiduguri.

A sakon da ya aika ta shafinsa na Twitter, Shugaba Buhari ya mika sakon ta'aziyyarsa ga iyalan wadanda lamarin ya ritsa da su da kuma sakon jaje ga wdanda suka ji rauni.

Shugaban ya kuma yi tir da kungiyar Boko Haram da ake zargin ita ta kai harin, yana mai cewa ''Kungiyar bata tsoron Allah kuma ayyukansu ba a kan dokar Allah suke ba.''

Hukumar ba da agajin gaggawa a Nigeria ta tabbatarwa da BBC cewa mutum huɗu ne suka mutu a hare-haren da aka kai jami'ar Maiduguri.

Wani jami'in hukumar bayar da agajin gaggawa a shiyyar arewa maso gabas ya ce mutum huɗu ne har da maharan suka mutu, yayin da wasu 17 suka jikkata a ciki har da masu munanan raunuka.

Hukumomin jami'ar sun ba da sanarwar ɗage jarrabawar ɗalibai da aka tsara za a fara a Litinin ɗin nan

Wannan ne dai karo na farko da ake zargin ƙungiyar Boko Haram da kai hari kai tsaye a jami'ar ta Maiduguri.