Mutum 37 sun mutu sakamakon faɗuwar jirgin Turkiyya

Turkish Cargo

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Jirgin ya faɗi ne da safiya cikin yanayin hazo da ya dusashe gari

Wani jirgin saman dakon kaya na Turkiyya ya yi hatsari a Kyrgyzstan, inda ya yi sanadin mutuwar mutum 37.

Jami'ai sun ce akasarin waɗanda suka mutu, jirgin ne ya faɗa musu suna ƙasa, jirgin ƙirar Boeing 747 TC-MCL ya yi ƙoƙarin sauka cikin yanayin hazo a filin jirgin Manas da ke wani waje mai nisan kilomita 25 a arewa da Bishkek babban birnin Kyrgyzstan.

Kananan yara sun rasa rayukansu kuma aƙalla gini 15 sun lalace a wani ƙauye da ke wajen filin jirgin.

Jirgin wanda ya so tsayawa a Manas na kan hanyarsa ne ta zuwa Istanbul a Turkiyya bayan ya taso daga Hong Kong.