Wata mai naƙuda ta haihu a bayan motar 'yan sanda

London
Bayanan hoto,

'Yan sanda sun kuma aika wa iyayen jaririyar saƙon taya murna

An haifi wata jaririya a cikin motar 'yan sanda, bayan motar iyayenta ta lalace a kan hanyarsu ta zuwa asibiti a London.

Mai jegon, Emily McBride da abokin zamanta Thomas Carson na kan hanyarsu ta zuwa asibitin koyarwa na jami'ar Royal Stoke lokacin da motarsu ta mutu.

'Yan sanda daga ofishin Staffordshire sun ɗauke su zuwa asibiti a bayan motarsu ta sintiri.

Sai dai, kafin Emily ta fita daga motar, sai ta haife jaririyarta wadda aka raɗawa suna Darcey.

Daga nan sai aka ƙarasa da mai jego da jaririyarta ɗakin karɓar haihuwa.

Mai jegon Ms McBride ta yaba wa 'yan sanda saboda kai ta asibiti a kan lokaci, a cewarta ba don 'yan sanda ba da ta haihu a cikin cunkoson motoci.