'Saudiyya ta janyo mutuwar mutum dubu 10 a Yemen'

Ko a Syria ma dai rikici ne tsakanin Saudiyya da Iran

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Saudiyya dai na gasa da kasar Iran

Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutum dubu 10 ne suka mutu, a yakin da ake yi, a kasar Yemen.

Kididdigar ta fara ne daga lokacin da hadakar sojin yaki da Saudiyya ke jagoranta ta shiga kasar, a 2015.

Saudiyya dai ta jagoranci gamayyar kasashen Larabawa guda takwas domin 'wanzar' da zaman lafiya.

Kasashen hadakar su ne Misra da Morocco da Jordan da Sudan da Hadaddiyar Daular Larabawa da Kuwait da Qatar da kuma Bahrain.

Har wa yau, kasashe kamar Djibouti da Eritria da kuma Somalia na kai hare-hare ta sama jifa-jifa.

Mai magana da yawun MDD, Farhan Haq, ya ce Majalisar za ta yi kokarin tsayar da rikicin ba tare da wani bata lokaci ba.

A jiya Litinin ne dai wakilin MDD na musamman, Isma'il Cheikh Ahmed ya gana da shugaban na Yemen, a wani mataki na tattauna yiwuwar sake farfado da batun tsagaita wuta.

MDD dai ta bayyana rikicin na Yemen da wanda ya fi kowanne muni ta fuskar daidaita mutane.

Wani Jami'in majalisar dinkin duniya ya ce, a yanzu haka, akwai mutane miliyan bakwai da ba su san inda za su samu abincin da za su ci ba.

Sannan kuma suna bukatar kariya daga azabtarwa da ma lafiyarsu.

Bayanan hoto,

Yadda wani bangare na birnin Sana'a yake

Sharhi, Usman Minjibir

Hadakar dai na kai wa dakarun mayakan sa-kai na kabilar Houthi mabiya mazhabar Shi'a kuma masu mara wa tsohon shugaban kasar, Ali Abdallah Saleh baya.

Kasar Iran ce dai ke goya wa 'yan kabilar ta Houthi baya.

Burin 'yan Houthi shi ne tunbuke shugaban mai ci wanda dan mazhabar Sunnah ne, Abdrabbuh Mansur Hadi wanda kuma shakikin kasar Saudiyya ne.

An dai kwashe shekaru uku ana gwabza yakin basasa a kasar, tun bayan da mayakan Houthi suka kwace iko da kasar a 2014, har ma suka fatattaki shugaba Abdrabbuh Mansur Hadi.

A 2012 ne dai Abdrabbuh Mansur Hadi ya ci zabe, a inda ya kawo karshen mulkin shugaba Ali Abdallah Saleh.

Kuma wannan al'amari bai yi wa mayakan na Houthi dadi ba bisa zargin yin ba dai-dai ba a zaben kasar.

Yemen dai na makwabtaka da gabashin Saudiyya mai albarkatun mai, a inda 'yan Shi'a ke da rinjaye.

Tsoron Saudiyyar dai shi ne idan 'yan Houthi mabiya Shi'a suka kwace ikon Yemen, to za su iya hada kai da 'yan Shi'a na gabashin Saudiyyar mai arziki man fetir.

Wasu dai na ganin rikici tsakanin Saudiyya da Iran na da alaka da siyasa ne ba addini ba.

Saudiyya dai na yi wa Iran kallon tana yi mata shiga-hanci da kudundune a kasashen Larabawa, bayan ita kuma ba Balarabiya ba ce.

Ana dai ganin rikici tsakanin kasashen biyu ne ya janyo har yanzu fadan da ake yi a Syria bai kare ba.

Iran dai na mara wa shugaba Bashir al-Asad baya, a inda ita kuma Saudiyya ke goyon bayan 'yan tawaye.

Wannan kuma na cigaba da janyo mutuwa da daidaitar fararen hula a kasar.

Yayin da Iran ke samun goyon bayan Rasha, ita kuwa Saudiyya babbar kawar Amurka ce.