An kama mutumin da ya kashe mutum 39 a Turkiyya

An kama Abdulkadir yana tare da dansa mai shekara hudu
Bayanan hoto,

Abdulkadir Masharipov lokacin da jami'an tsaro suka kama shi

Kafofin watsa labaran kasar Turkiyya, sun ce, an kama mutumin da ake zargi da kai hari kan gidan wani rawa, a lokacin shagulgulan bikin sabuwar shekara, a Istanbul.

An ta jin hayaniya yayin kiciciyar kama mutumin mai suna Abdulkadir Masharipov wanda dan asalin kasar Uzbekistan ne, lokacin wani samame da aka kai a farfajiyar wani gida, a birnin na Istanbul.

An kuma ce an sami Abdulkadir tare da dansa mai shekara hudu, a wani gida mallakar wani dan kasar Kyrgyztan.

Mutane 39 ne dai suka mutu yayin harin da ake zargi Abdulkadir ya kai a daren ranar sabuwar shekarar nan.