Ministocin Jammeh sun sauka daga mukamansu

Yahya Jammeh

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

ECOWAS ta ce dole Jammeh ya sauka daga mulki

Manyan ministoci hudu sun mika takardun ajiye ayyukansu ga shugaban kasar Gambia Yahya Jammeh a daidai lokacin da shugaban ke ci gaba da shan alwashin kin sauka daga mulki, a cewar shafin intanet na Fatu wanda ke goyon bayan 'yan hamayya.

Shafin ya ruwaito cewa ministocin harkokin kasashen waje da na kudi da na ciniki - Neneh Macdouall-Gaye, Abdou Kolley da Abdou Jobe sun ajiye ayyukansu ranar Litinin.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce ministan muhallaci ma ya sauka daga mukaminsa.

A makon jiya ne ministan watsa labarai Sheriff Bojang da na wasanni Alieu Jammeh suka sauka daga mukamansu, a cewar shafin na Fatu.

Dubban mutane ne ke ci gaba da tsere wa daga kasar zuwa makwabciyarta Senegal, yayin da wasu ma ke tafiya Guinea-Bissau saboda fargabar da ake yi cewa za a yi rikici idan Mr Jammeh ya ki mika mulki ranar Alhamis.

Mutumin da ya yi nasara a zaben, Adama Barrow, wanda yanzu ke kasar Senegal saboda shawarar da shugabannin ECOWAS suka ba shi, ya sha alwashin hawa mulki ranar Juma'a.

Da farko dai Mr Jammeh, wanda ya shafe shekara 22 a kan mulki, ya amince da shan kaye amma daga bisani ya ce ba zai sauka ba saboda an tafka magudi a zaben da aka yi a kasar a watan Nuwamba.