''Yan Afirka sun fi morar Bush a kan Obama'

Bush ya gaji Clinton

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Obama ne ya gaji Bush

Masu sharhi kan siyasar Amurka sun ce tsohon shugaban kasar, George Bush ya fi Barack Obama ga nahiyar Afirka.

Umar Sa'idu Tudunwada wanda dan jarida ne kuma mai sharhi kan siyasar Amurkar, ya ce idan kwatanta Bush da Obama dangane da abin suka yi wa nahiyar Afirka, to Bush yana gaba da Obama.

Ya ce "duk da cewa Barack Obama dan Afirka ne amma Afirkar ta fi cin moriyar Bush a kan Obaman."

"Yakin neman zaben Obama ya takaita ga Amurka ba Afirka ba." In ji Tudun Wada.

Ya kuma kara da cewa babu wani shiri da Obama ya yi wa Afirka da za a ce 'yan nahiyar na cin moriya.

Amma ya ce Bush ya fito da tsare-tsare kamar raba wasu kasashen nahiyar da yaki da kuma shirin samar da waraka ga cuta mai karya garkuwar jiki.