Kun san hare-haren da soji suka kai bisa kuskure?

  • Nasidi Adamu Yahya
  • BBC Hausa
Wata yarinya da ta jikkata

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Fiye da mutum 100 ne suka jikkata wadanda ke samun kulawa a asibitoci daban daban

Kisan da wani jirgin saman sojin Najeriya ya yi wa wasu 'yan gudun hijira da ma'aikatan bayar da agaji sakamakon harin da ya kai musu bisa kuskure ranar Laraba a kauyen Rann da ke jihar Borno ba shi ne karon farko da ake samun irin wannan matsala a kasashen duniya ba.

Ita dai rundunar sojin Najeriya ta ce jirgin yakin ya kai hari kan mutanen ne bisa zaton cewa 'yan kungiyar Boko Haram ne, inda ya kashe akalla mutum 70.

Sai dai kungiyar Red Cross mai bayar da agaji ta ce harin ya yi matukar dimauta ta, tana mai cewa "irin wannan kuskuren abu ne da ba za a taba amicewa da shi ba."

A baya dai, an samu irin wadannan matsaloli inda jiragen yakin soji ke kai hari bisa kuskure kan farar-hula.

'Masu makoki a Nijar'

A watan Fabrairun shekarar 2015, wani jirgin yaki ya kashe mutum 37 da ke zaman makoki bisa 'kuskure' a yankin Abadam na Jamhuriyar Nijar.

Mataimakin magajin garin Abadam, Ibrahim Ari wanda ya tabbatar wa da BBC aukuwar lamarin, ya ce fiye da mutum 20 kuma sun jikkata.

Jirgin dai na dakarun kawance da suka hada da na Najeriya da Nijar da kuma Chadi ne da ke kai farmaki kan maboyar 'yan kungiyar Boko Haram ta sama da ta kasa.

'Saudiyya ta kashe 'yan Yemen'

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Jiragen saman Amurka sun sha kashe farar-hula da gangan

A can kasar Yemen ma, wasu jiragen saman yaki na kawancen da Saudiyya ke jagoranta, sun jefa bom a kan wani taron masu zaman makoki a watan Sataumbar bara, wanda ya yi sanadin mutuwar mutum 140, da raunata fiye da mutum 500.

Hukumar da ta yi bincike kan lamarin ta ce wani babban jami'in sojin Yemen ne ya bayar da bayanan da ba su da inganci inda ya ce 'yan tawayen Houthi ne ke taro a lokacin.

Kuma akwai bukatar a dauki matakin gaggawa a kansu, lamarin da ya sanya aka yi kuskuren kashe far-hular.

'Kanwa uwar gami'

Masu sharhi a kan sha'anin tsaro na ganin cewa hare-haren da jiragen yakin Amurka suka kai bisa 'kuskure kan farar-hula a kasashe daban-daban ba za su lissafu ba.

Sau da dama dai jiragen na kai hare-haren ne da niyyar kashe 'yan kungiyoyin masu tayar da kayar baya irin su IS da A-Qaeda da makamantan su.

Wasu daga cikin hare-haren da suka kai kan wani asibitin kungiyar likitoci ta MSF da ke birnin Kunduz na kasar Afghanistan a watan Yunin 2015 wanda ya yi sanadin mutuwar mutum 32, cikin su har da kananan yara uku.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Hare-haren da jiragen yakin Amurka suka kai Iraqi sun yi barna mai matukar yawa

A lokacin da ya je gaban majaliasar dattawan Amurka domin yi mata jawabi kan harin, babban kwamandan sojin kasar a Afghanistan na wancan lokacin, Janar John Campbell, ya amince cewa sun kai hari kan asibitin ne bisa kuskure.

Ya kara da cewaa, "Ba za mu sake kai hari kan asibitoci da gangan ba".

Sai dai a watan Yuli na shekarar, wani hari ta sama da jiragen yakin Amurka suka kai a wani wurin binciken abubuwan hawa a lardin Logar da ke kudancin Kabul ya yi sanadin mutuwar akalla sojojin Afghanistan 14.

'Yan kungiyar Taliban ne dai ke da ikon lardin.

A watan Janairu na wancan shekarar, jiragen yakin Amurka marasa matuka sun kai hari a kan iyakar Afghanistan da Pakistan inda suka kashe wasu mutum uku da aka yi garkuwa da su, cikin su har da wani dan kasar Italiya, Giovanni Lo Porto da wani Ba'amurke ma'aikaci, Warren Weinstein.

Dakarun sojin Amurka sun ce sun yi tsammani babu farar-hula a wurin da suka kai harin.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Farar-hula sun shiga uku sakamakon irin wadannan hare-hare

Iraqi da Syria

A shekarar 1991, lokacin yakin tekun Fasha, jiragen yakin Amurka suka kai hari kan wani gida da ke Amiriyah kusa da Baghdad, inda aka kashe farar-hula 408 a wani gida.

Dakarun sojin Amurka sun ce an kai harin ne saboda zargin da suka yi cewa tsohon shugaban kasar Saddam Hussein na yin amfani da mutanen gidan ne domin su zame masu garkuwa.

Kazalika sojin na Amurka sun kashe mutane da dama a Syria a irin wadannan hare-hare, inda ko da a watan Yunin 2016 wani hari da jiragen yakin Amurkar ya kashe farar-hula 85 a Manbij da ke arewacin Syria bayan ya yi tsammanin mayakan kungiyar IS ne.

Baya ga Amurka, kasashe irin su Rasha da Birtaniya sun kai irin wadannan hare-hare da suka yi sanadin mutuwar farar-hula da dama.