Me ya sa shugabannin Afirka ke tsoron mulkin Trump?

US
Bayanan hoto,

Wasu Amurkawa da ke zanga-zanga don nuna adawarsu kan zaben Donald Trump

Tun a lokacin da sabon shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump ya samu nasara a zaben da aka gudanar, 'yan Afrika da dama ciki har da wasu shugabannin kasashen nahiyar ke nuna fargaba a kan yadda zai gudanar da mulkinsa, duba da irin kalaman nuna kin jinin wadanda ba Amurkawa ba da ya dinga yi lokacin yakin neman zabe.

Ana ganin mulkin Trump ka iya janyo sanewar dangantaka tsakanin Afirka da Amurka, bisa la'akari da kalamansa na mayar da hankali wajen bunƙasa al'amuran cikin gida.

Hausawa kan ce ba a hana ma-ba-da rago, fata. Ana ganin yadda rinjayen 'yan Afirka ba su goya wa Trump baya a zabensa ba, su ma kuwa ba lallai ne su samu fuskar wajen tura muradan kasashensu a gwamnatinsa ba.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Shugaban Namibia Greingob na ganin kowa tasa ta fisshe shi

Shugabannin ƙasashen Afirka kamar na Namibia, Haggy Geingob na mamaki game da salon zaɓen Amurka wadda ya kai Trump kan mulki ta hanyar rinjayar da ƙuri'ar wakilai a kan cincirindon masu zaɓe.

Manufofin hulɗa da ƙasashen wajen Amurka ka iya mayar da Afirka kurar-baya.

Abubuwan da ke faruwa a Sudan ko Kenya ko jamhuriyar Dimokradiyyar Congo ko Somaliya da ma sauran kasashen Afirka masu fama da rikici ba lallai ne su damu shugaba Trump ba. Don haka za a yi zaman nan da masu iya magana ke cewa karena ba ni korarka, ba ni ba ka abuna.

Afirka ta ci moriyar ɗumbin tagomashi a gwamnatocin shugabannin Amurka da suka haɗar da George Bush da Bill Clinton da kuma Barack Obama.

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Shugaba Ellen Johnson Sirleaf ta Liberia da Muhammadu Buhari na Nijeriya da kuma shugaban Senegal Marky Sall

Hulda ta fuskar inganta tsaro da harkokin soja tsakanin kasashen Afirka da Amurka ta hanyar rundunar sojan Amurka mai kula da Afirka (Africom) wadda aka kafa a shekara ta 2007 ka iya yin rauni. Rundunar ta taimaka wajen kyautata dangantakar ayyukan soja tsakanin Amurka da Tarayyar Afirka da sauran rundunonin soja na kungiyoyin kasashen yankuna da ma daidaikun kasashe.

Najeriya wadda ta samu tallafin soja mai yawa daga Amurka don yaƙi da kungiyar Boko Haram ta aika saƙon taya Donald Trump murnar cin zaɓe, kuma shugabanta Muhammadu Buhari wanda wasu suka yi iƙirarin cewa gwamnatinsa ta taimaka wa yaƙin neman zaɓen Hillary Clinton duk da yake babu wata shaida da ke nuna hakan, ya ci alwashin yin aiki tare da sabon shugaban.

Dokar ba da dama da bunkasa Afirka mai suna AGOA wadda aka ɓullo da ita a shekara ta 2000 ta taimaka wa 'yan kasuwa da matsakaitan masana'antun Afirka shiga kasuwar Amurka ba tare da biyan haraji ba.

Bayanan hoto,

Donald Trump ya yi alkawarin kawo sabbin manufofi wadanda wasu ke gani ba za su yi wa Afirka dadi ba

A watan Yunin 2015, shugaba Barack Obama ya tsawaita dokar don ta ci gaba da aiki har zuwa shekara ta 2025, sai dai tana iya fuskantar nakasu bisa la'akari da ganin take-taken Trump na kakkare komai, ba kuma lallai ne ya sake tsawaita dokar ba.

Amurka na kashe maƙudan kuɗi a matsayin tallafi ga kasashen Afirka ta fuskar tattalin arziki da samar da abinci da bunkasa kwarewa da kula da lafiya da takaita yaɗuwar cuta mai karya garkuwar jiki.

A matsayinsa na dan kasuwa, Trump zai so ganin tallafin da Amurka ke bai wa ƙasashen Afirka kamar Djibouti da Malawi na cuɗe-ni-in-cuɗe-ka ne maimakon taimako kawai. Haggy Geingob na ganin hakan zai sakar wa ƙasashen Afirka mara su yi salon mulkin da suka ga ya fi dacewa da su. A cewarsa Afirka ta girma don haka za ta iya shata wa kanta alƙibla.

Shirye-shirye irinsu Power Africa Act don bunƙasa samar da lantarki a Afirka da na Food Security Act don wadata ƙasashe da abinci da shirin bunƙasa ƙwarewar matasan Afirka ta yadda za su san makamar shugabanci wanda ake yi wa take da YALI, da tallafi kan fannin bunkasa lafiya da ilmin 'ya'ya mata da shirin gaggawa na shugaban ƙasa don takaita cuta mai karya garkuwar jiki PEPFAR, wanda George W Bush ya ƙirƙiro ba lallai ne a yanzu su samu kulawar da suka samu a baya ba.

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Dubban 'yan Afirka ne suke sanya rayuwarsu cikin kasada wajen tsallaka teku don zuwa ci-rani a kasashen Turai

Akasarin 'yan Afirka na tababa a kan an ya gwamnatin Trump ba za ta kori 'yan ci ranin Afirka ba, ta haramta wa musulmi shiga ƙasar? Ko Amurka za ta ci gaba da zama haɓar taguminsu kamar yadda abin yake tsawon lokaci a baya?

'Wani hanin ga Allah baiwa ne'

Wasu na ganin mulkin Trump ka iya zama alheri ga Afirka wajen yi musu kaimi don ƙarfafa huldarsu da ƙasashe irinsu China wadda ba ruwanta da tsirfar ƙaƙaba musu mulkin dimokradiyya kafin ta yi ƙawance da su ko kuma su yi wata hulɗar cinikayya.

Idan abin da ake hasashe ya tabbata, gwamnatin Donald Trump ta mayar da hankalinta cikin gida, ƙasashen Afirka za su samun sassaucin katsalandan cikin harkokinsu.

Ƙasashen Afirka a yanzu suna iya mayar da hankali zuwa cikin gida don bunƙasa tattalin arziƙinsu maimakon jiran tallafin da ba lallai ne su same shi a zamanin mulkin Trump ba.

Wasu 'yan Afirka kamar shugaban Namibia, Haggy Geingob na ganin tsarin Amurka shi ne gaba da kowa kuma ƙasaitacciyar ƙasa kamar Amurka mai tsayayyen salon dimokradiyya, za ta biyar da duk Trump kan tsarin da aka girka tun ainihi.

Donald Trump dai shi ne shugaban Amurka na 45.