Celta ta ci Madrid 2-1 a Bernebue

Copa del Rey

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

A makon jiya ne Sevilla ta doke Madrid, bayan da ta yi wasanni 40 a jere ba tare da an ci ta ba

Real Madrid ta yi rashin nasara a hannun Celta de Vigo da ci 2-1 a wasan daf da na kusa da karshe a gasar Copa del Rey da suka kara a Bernebeu a ranar Laraba.

Iago Aspas ne ya fara ci wa Celta kwallo a minti na 64, daga baya ne ne Madrid ta farke ta hannun Marcelo Vieira Da Silva.

Daga baya Celta ta kara cin kwallo ta biyu ta hannun Jonny.

A daya wasan na biyu kuwa Alcorcon ce ta yi rashin nasara a hannun Deportivo da ci biyu da babu ko daya.

Real Madrid za ta ziyarci Celta a wasa na biyu a ranar 22 ga watan Janairu, a kuma ranar ce Deportivo za ta karbi bakuncin Alcorcon.

Sauran wasannin daf da na kusa da karshe za a fafata ne tsakanin Athletico de Madrid da Eibar da kuma kece raini tsakanin Real Sociedad da Barcelona ranar Alhamis.