Juventus ta ci gaba da jan ragamar teburin Serie A

Gasar cin kofin Italiya

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Dybala ya ci kwallaye biyar a gasar Serie A ta bana

Kungiyar Juventus ta ci gaba da zama ta daya a kan teburin gasar Italiya, bayan da ta ci Lazio 2-0 a fafatawar da suka yi a Turin a ranar Lahadi.

Juve ta ci kwallon farko ne tun daga yadi na 20 ta hannun Paulo Dybala, daga baya ta kara ta biyu ta hannun Gonzalo Higuain.

Higuain ya kara cin kwallo amma alkalin wasa ya ce ya yi satar gida kafin ya saka ta a raga, amma tuni Juve ta hada maki ukun da take bukata a fafatawar.

Juventus mai rike da kofin Serie A na bara ta bayar da tarar maki biyar tsakaninta da Roma mai take matsayi na biyu, wadda za ta kara da Cagliari da yammacin Lahadi.