Obama ya gargadi Trump kan cire wa Russia takunkumi

Donald Trump, mai alaka da Rasha ne zai gaje shi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Obama zai bar fadar White House ranar Juma'a

Shugaban Amurka mai barin gado, Barack Obama, ya yi wa magajinsa, Donald Trump kashedin cewa ya kula da Rasha.

A wani jawabinsa na karshe ga manema labarai, a matsayinsa na shugaban kasa, mista Obama, ya ce, ka da magajin nasa ya kwaye wa Rasha takunkumin da Amurkar ta kakaba mata.

Sai dai kuma mista Obaman ya bayar da sharadi cewa har sai idan Rashar ta amince ta fita daga kasar Ukrain.

Obama ya kara da cewa shugaban Rashar, Vladimir Putin ne da kansa ya sanya alaka ta yi tsami tsakanin kasar tasa da Amurka.

"Zan iya cewa tun bayan da shugaba Putin ya yi kome a matsayin shugaban kasa, ake samun wani yanayi na nuna kin jinin Amurka irin wanda ya faru a lokacin yakin cacar baka." In ji Obama.

Zargin kutse da hukumomin tsaron Amurka suka yi wa Rasha, shi ne batun da ya kara sanya alaka ta yi tsami tsakanin kasashen biyu.

An dai zargi Rasha da yin kutse cikin tarin wasikun imel na 'yar takarar shugabancin Amurkar ta jam'iyyar Democrat, Hillary Clinton.