'Dole musulman duniya su tsoma baki kan rikicin Myanmar'

Rohingya

Asalin hoton, MUNIR UZ ZAMAN/AFP

Bayanan hoto,

Dubban 'yan Rohingya su gudu zuwa zangon 'yan gudun hijira a Bangladesh tun watan Oktoba

Firai ministan Malaysia Najib Razak ya yi kira ga kasashen musulmai da su shige gaba wajen ganin an dauki mataki don kwato musulmai 'yan Rohingya na kasar Myanmar daga halin da suke ciki.

Mista Razak ya yi wadannan kalamai ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a wajen bude taron kungiyar bunkasa hadin kan kasashen musulmai, OIC da ake yi a birnin Kuala Lumpur.

Kungiyar OIC tana da mambobin kasashe 57 wadanda yawan jama'arsu musulmai ne.

Kungiyar tana wani taron gaggawa ne domin tattauna matsalolin agaji da musulman Myanmar ke fuskanta.

An yi kiyasin cewa musulmai 'yan Rohingya 65,000 ne suka tsere daga jihar Rakhine tun lokacin da sojojin Burma suka kaddamar da shirin yaki da ta'addanci mai zurfi a watan Oktobar 2016.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Masu zanga-zanga a Malaysia da kuma sauran wurare sun zargi Aung San Suu Kyi

Da yake bayyana halin da ake ciki, Mista Najib ya ce, ''Mutane da dama sun rasa rayukansu a Myanmar. Wasu da yawa sun shiga tarkon mutuwa, wasu kuma da suka sha da kyar sun ga cin zarafi da zalunci kala-kala. Wannan ne dalilin da ya sa ba za mu yi shiru mu zuba id a ci gaba da wannan zalinci ba.''

Me yake faruwa a jihar Rakhine?

Bayan hare-haren da aka kai wa sojoji a watan Oktoba a gundumar Maungdaw, sai hukumomi suka kaddamar da yaki da ta'addanci, wanda masu sukar lamari suka ce ya jawo dumbin kashe-kashe, da fyade da lalata kauyukan 'yan Rohingya.

Sai dai gwamnatin Myanmar ta yi watsi da sukar ta kuma ce 'yan Rohingya ne suka kona kauyukansu da kansu don su jawo hankalin kasashen duniya.

Gwamnatin ta kuma hana kungiyoyi masu zaman kansu da kafafen yada labaran kasashen waje da suka hada da BBC shiga yankin don yin bincike kan zargin da ake mata.

Su waye'yan Rohingya ne?

Mutane da dama na daukar musulmai 'yan Rohingya da aka kiyasta yawansu ya kai miliyan daya a matsayin 'yan ci rani ne daga Bangladesh.

Gwamnatin ta hana su shaidar zama cikakkun 'yan kasa duk da cewa suna zaune a yankin shekaru aru-aru.

Rikicin kabilanci da aka yi a jihar Rakhine a shekarar 2013 ya yi sanadin mutuwar mutane da dama ya kuma raba fiye da mutum 100,000 da muhallansu.

Suna fuskantar wariya da kuma gallazawa.