Barack Obama ya yi wa fursunoni 330 afuwa

Donald Trump ya sha alwashin sake waiwayar wasu tsare-tsaren Obama

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

A ranar Juma'a ne za a rantsar da Donald Trump

Shugaban Amurka mai barin gado, Barack Obama, ya yi afuwa ga fursunoni 330, a ranarsa ta karshe, a fadar White House.

Mafi yawancinsu mutanen da aka yi wa afuwar sun aikata laifukane masu nasaba da safarar miyagu kwayoyi.

Wannan ce dai wata afuwa da aka taba yi mafi girma a rana daya, a tarihin kasar.

Kuma a tsawon shekaru takwas da Obama ya kwashe yana mulki, ya rage girman hukuncin da aka yankewa mutane 1715.

Hakan kuwa ya nuna cewa shi ne shugaban Amurkar na farko da ya rage girman hukuncin da aka yankewa mutane masu tarin yawa.

A ranar Juma'a ne dai za a rantsar da magajin Obama wato Donald Trump, a matsayin shugaban Amurka na 45.