Amurka: zanga-zanga ta barke bayan rantsar da Trump

Dandazon Masu zanga-zangar kin jinin Trump

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Zanga-zangar ta bazu zuwa wasu biranen kasar kamar su San Francisco da Atlanta

'Yansanda a birnin Washington sun dauki sa'o'i suna arangama da daruruwan masu zanga-zangar kin jinin sabon shugaban Amurka Donald Trump jim kadan bayan rantsar da shi.

An yi zanga-zangar ne a wasu sassan birnin cikin lumana sabanin kusa da inda aka yi bukin rantsarwar inda suka farfasa tagogi shaguna daban-daban cikin har da Starbucks, da Bankin Amurka da kuma McDonald suna sukar tsarin jari hujja da kuma Trump.

'Yansandan dai sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye da kuma gurneti wajen tarwatsa su kuma suka sun kama mutane har 90.

Zanga-zangar ta fara ne kimanin awa daya kafin bukin rantsarwar amma sai ta kara kamari sa'o'i bayan rantsar da shin indan yawan masu zanga-zangar ya karu zuwa kusan dubu daya.