Dusar kankara ta mamaye wani otel a Italiya

Asalin hoton, CNSAS
Har yanzu ana cigaba da ciro mutane daga cikin dusar kankarar
Rahotanni daga Italiya na cewa an kara ciro karin wasu mutum uku daga dusar kankara da kuma baraguzan ginin da ya shafe wani otel a ranar Laraba.
Tunda farko a ranar Jumma'a, masu aikin ceto sun ciro wasu mutum shida da ransu, hudu yara biyu kuwa manya ne.
Mutanen dai sun kasance abinne a karkashin baraguzan gini da kuma dusar kankarar fiye da sa'oi 40, kuma an ciro su a raye sakamakon wata kafa da suka samu inda suke shakar isaka daga otel din.
Masu aikin ceton dai sun ce za su cigaba da aiki har sai sun gano kowa.
Akwai dai fiye da mutane da dama da har yanzu ba a kai ga gano su ba.