Ba zan koma Gambia ba sai komi ya daidaita - Barrow

Adama Barrow ya na shan rantsuwa

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

An rantsar da Barrow ne a ofishin jakadancin Gambia da ke kasar Senegal

A yayin da Yahya Jammeh ya fice daga Gambia, sabon Shugaban kasar Adama Barrow ya ce ba zai koma kasar ba har sai sojojin kasashen wajen da ke can sun ce ya yi hakan.

Adama Barrow na fakewa ne a makwabciyar Senagal inda can ne ma aka rantsar da shi bayan yunkurin da kungiyar Ecowas ta yi na ciwo kan Jammeh ya sauka ya ci tura ranar Alhamis.

A cikin wata hira da BBC, sabon shugaban ya ce zai koma kasar ba da jimawa ba, amma yanzu yana kan tattaunawa da kungiyar ta kasashen yammacin Afrika.

''Kamar yadda kuka sani, sojojin kasashen waje na cikin wannan kasar, ke nan dole sai sun yi sanarwar cewa komai ya daidaita kafin in koma'' in ji shi.

Barrow ya ce idan ya koma, tattalin arziki shi ne abu na farko da zai fara dubawa, kodayake ya ce akwai batutuwa da dama da ke bukatar a ba su fifiko.