India: Hadarin jirgin kasa ya kashe mutum 36 a Andhra Pradesh

Masu aikin ceto sun ce akwai yi wuwar adadin wadanda suka mutu ya karu
Bayanan hoto,

Hadarin jirgin kasa a India ba wani sabon abu bane saboda lalacewar layukan dogo

Akalla mutum talatin da shidda sun rasa rayukansu, yayin da wasu kusan dari kuma suka jikkata bayan da wani jirgin kasa ya yi hadari a jihar Andhra Pradesh da ke kudu maso gabashin India.

Rahotanni sun ce taragai bakwai da kuma injin jirgin wanda ya taso daga Jagdalpur zuwa Bhubaneswar suka kauce hanya.

Akwai dai mutane da dama da suka makale a cikin tarkacen jirgin, kuma masu aikin ceto sun ce akwai yiwuwar adadin wadanda suka mutu zai iya karuwa.

Hadarin jirgin kasa dai ya zama jiki a India saboda layukan dogon duk sun tsufa.

Ko a watan Nuwambar shekarar da ta gabata, fiye da mutum dari da arba'in ne suka mutu a jihar Uttar Pradesh sakamakon hadarin jirgin kasa.