Trump: Da shugaban Mexico zan fara ganawa a fadar gwamnati

Trump ya bayyana cewa da shugaban kasar Mexico zai fara ganawa a fadar gwamnatin Amurka
Bayanan hoto,

Trump ya bayyana cewa da shugaban kasar Mexico zai fara ganawa a fadar gwamnatin Amurka

Mai magana da yawun fadar gwamnatin Amurka ya sanar da cewa shugaban kasar Mexico, Enrique Pena Nieto, shi ne zai kasance shugaban kasar da zai fara ganawa da shugaba Trump a fadar.

Ana kyautata tsammanin za su yi wannan ganawa ne a karshen watan da muke ciki.

A lokacin yakin neman zaben Amurka dai, Mr Trump ya soki 'yanci ranin Mexico inda har ya yi alkawarin cewa zai gina katanga a tsakanin kasashen, kuma Mexicon ce za ta biya kudin.

Sai dai kuma wani wakilin BBC ya ce duk da wadannan kalamai na Mr Trump, Mexico takasance babbar abokiyar huldar Amurka, inda suke kasuwancin biliyoyin daloli a duk shekara a tsakaninsu.