"ECOWAS ba za ta ba Jammeh kariya ba"

Gambia

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Yanzu za a iya binciken zarge-zargen aikata laifukan take hakkin jama'a da ake yi wa Mista Jammeh

Bayan wasu sa'o'i da tsohon shugaban Gambia, Yahya Jammeh ya fice daga kasar, ministan harkokin wajen Senegal ya ce shugabannin ECOWAS ba su amince da ba tsohon shugaban kariya ba.

Daga farko rahotanni sun ce kungiyar ECOWAS da Tarayyar Afirka da kuma Majalisar Dinkin Duniya sun amince su ba Mista Jammeh kariya, a matsayin wani bangare na yarjejeniyar da aka cimma ta saukarshi daga mulki.

Sai dai ministan harkokin wajen Senegal, Mankeur Ndiaye ya ce shugabannin kasashen ECOWAS ba su amince da ba Mista Jammeh wata kariya ba.

Ana zargin tsohon shugaban Gambiyan ne da aikata manyan laifukan take hakkin dan Adam a shekaru ashirin da biyu da yayi yana shugabancin kasar.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Tsohon shugaban kasar Gambia Yayha Jammeh ya fice daga kasar zuwa Guinea

Tsohon Shugaban kasar Gambia Yahya Jammeh ya fice daga kasar ne bayan ya amince ya mika mulki ga Adama Barrow, wanda ya ka da shi a zaben shugaban kasa na watan jiya.

Da tsakar daren ranar Asabar ne Jammeh ya sanar da cewa zai sauka daga kan mulki bayan kwashe shekaru 22 yana mulkin kasar.

Ya dai bar kasar cikin wani karamin jirgin sama a filin jirgin birnin Banjul tare da matarsa da kuma shugaban kasar Guinea Alpha Conde.

Bankwana

Wakilin BBC a Banjul Alaistair Leithead ya ce Mista Jammeh ya isa filin jirgin saman Banjul ne a cikin wani jerin gwanon motoci.

Bayan da ya fito ya tsaya ya saurari kidan 'yan badujala na sojojin kasar a karo na karshe sannan ya juya yana tafiya kan wata jar darduma zuwa cikin wani karamin jirgi da ba ya da rubutu a jikinsa.

Daga nan sai ya taka tsanin shiga jirgin sannan ya juyo ya dagawa taron jama'ar da suka rako shi hannu kuma ya sumbaci alkur'aninsa kafin ya shige cikin jirgin.

Muhimman mutane da yawa da kuma magoya bayansa da suka yi dafifi a wajen filin jirgin sun shiga wani hali na bacin rai bayan ganin shugabansu ya tafi bayan kwashe shekaru 22 kan mulki.

Sai dai kuma wasu da yawa a cikin kasar ta Gambia sun yi murna da ganin karshen abin da suke ganin mulkin kama-karya ne wanda bai mutunta hakkin bil'adama da kuma 'yancin fadin albarkacin baki sai can ba a rasa ba.