Seville ta daura aniyar kamo Madrid a teburin La Liga

Gasar cin kofin La Liga

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Vicente Iborra ya ci wa Sevilla kwallaye biyar a bana

Sevilla sai kara matsa wa Real Madrid lamba take yi domin karbe mataki na daya a kan teburin La Liga, bayan da ta ci Osasuna 4-3 a wasan mako na 19 da suka yi a ranar Lahadi.

Osasuna ce ta fara cin kwallo ta hannun Sergio Leon daga baya Sevilla ta farke ta hannun Vicente Iborra tun kafin a je hutun rabin lokaci.

Bayan da aka dawo daga hutu Osasuna ta ci ta biyu bayan da Vicente Iborra ya ci gida, haka dai Vicente Iborra ne ya sake farke wa Sevilla kwallo na biyu.

Franco Vazquez ne ya ci wa Sevilla kwallo na uku sannan Pablo Sarabia ya ci mata na hudu.

Sai dai kuma Osasuna ta zare kwallo daya daf da za a tashi daga fafatawar ta hannun Kenan Kodro.

Real Madrid wadda ta doke Malaga a ranar Asabar tana da maki 43 a kan teburin La Liga da kwantan wasa daya a matsayi na daya, yayin da Sevilla ke mataki na biyu da maki 42.