Jammeh ya yi awon gaba da dala Miliyan 11 - Barrow

Adama Barrow

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Har yanzu dai Adama Barrow bai koma Gambia ba.

Wani mashawarcin sabon Shugaban Gambia Adama Barrow ya ce fiye da dalar Amurka miliyan 11 ne ake jin sun salwanta daga asusun gwamnati sakamakon ficewar tsohon shugaban Yahya Jammeh daga kasar.

Mia Ahmad Fatty ya shaida wa manema labarai a Dakar - babban birnin kasar Senegal - cewa kwararru kan harkokin kudade na can na kokarin gano ainihin yawan kudaden da suka bata.

Ya ce a yanzu kasar na cikin wani hali na kaka-ni-ka-yi saboda kusan ba ta da komai a baitil malinta bayan da ya kwashi fiye da dalla miliyan 11 a cikin makonni biyun da suka gabata.

Mr. Fatty ya yi zargin cewa tsohon shugaban ya yi amfani da kudin ne wajen sayen wasu kayayyakin alfarma da zai yi amfani da su bayan saukarsa mulki.

Kodayake dai ba a iya tabbatar da hakan ta wata majiya mai zaman kanta ba kawo yanzu, wakilin BBC a birnin Banjul ya ce an ga wani jirgin saman dakon kaya na kasar Chadi ya kwashi motocin alfarma da wasu kayayyaki a madadin Yahya Jammeh a daren da ya bar kasar.