Syria: Ana gagarumar tattaunawar sulhu a Kazakhstan

Wasu kananan yaran da rikicin ya raba da gida

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Miliyoyin 'yan Syria ne ke zauna a sansanoni 'yan gudun hijira

An soma wata gagarumar tattaunawar kawo zaman lafiya da manufar warware rikicin Syria a Astana babban birnin Kazakhstan.

Masu halartar tattaunawar na da goyon bayan kasashen Rasha da Iran masu goyon bayan gwamnatin Syria da kuma Turkiyya wadda ke goyon bayan 'yan tawaye.

Wannan dai shi ne karon farko tun bayar barkewar rikicin shekaru shidan da suka wuce da wata tawagar wakillan kungiyoyin 'yan tawaye zalla ke tattaunawar sulhu da gwamnati.

Sai dai ba a bai wa kungiyar IS iznin halartar tattaunawar ba.

Jakadan Majalisar Dinkin Duniya, Steffan de Mistura, ya ce taron farar dabara ce kuma ya ce yana fatan zai taimaka wa tattaunawar zaman lafiyar da za a yi a birnin Geneva watan gobe.

A cikin shekaru 6 da aka kwashe ana yakin basasa a kasar, fiye da mutane dubu 300 ne suka rasa rayukansu wasu kuma miliyan 11 suka kaurace wa gidajensu.